¡Acompáñanos a viajar por el mundo de los libros!
Añadir este libro a la estantería
Grey
Escribe un nuevo comentario Default profile 50px
Grey
Suscríbete para leer el libro completo o lee las primeras páginas gratis.
All characters reduced
Mafarkin Farin Ciki - Zaɓar Soyeyya A Kan Tsoro - cover

Mafarkin Farin Ciki - Zaɓar Soyeyya A Kan Tsoro

Ken Luball

Editorial: Tektime

  • 0
  • 0
  • 0

Sinopsis

“Wanda ya dubi waje, zai yi mafarki. Wanda dubi ciki, zai farka.” - Carl Jung Mafarkin Farin Ciki; Zabar Soyeyya a kan Tsoro littafin na hudu cikin “Jerin Littattafai Hudu na Farkarwa”. Wannan littafi ya bayyana kura-kuran hanyoyi da yawa cikin rayuwa wanda zamu iya dauka da ta yaya zamu sami kwanciyar hankali na gaske da manufa a cikin rayuwar mu. Idan dangantakar mu da duniya da ke kewaye damu ya ginu ne ta madubiyar rinjaye da tsoro, tafiyar mu ta rayuwa sau da yawa zata kasance cikin kadaici da zalunci. Matsalolin mu basu da iyaka, kayan mu nada nauyi, Sau da yawa yakan jagorantar mu zuwa mikakkun shinge, bamu kariya daga motsin rai mai rauni. Duk da haka wadannan shingen su suke ware mu kuma daga kowane abu na daban dake kewaye da mu, ciki har da asalin kanmu. Mafarkin Farin ciki littafi ne na Ruhaniya dake bayyana yadda zamu rungumi soyeyya a kan tsoro, dakatar da neman ma”ana da farin ciki ta ayyukan waje da dangantaka a cikin duniya; Sabanin haka, neman shi daga ciki.

PUBLISHER: TEKTIME
Disponible desde: 17/09/2022.

Otros libros que te pueden interesar

  • 4 – Hour Interviews in Hell - HAUSA EDITION - School of the Holy Spirit Series 12 of 12 Stage 1 of 3 - cover

    4 – Hour Interviews in Hell -...

    Yemi Bankole

    • 0
    • 0
    • 0
    4 – Tattaunawar Sa’a a Jahannama
    
    Wannan sako ne daga kasa mai nisa. Ana nufin duniya; miliyoyin sun karanta; masu tawali'u sun gaskata; masu hikima suka yi addu'a game da shi. Ko da yake, za a haye teku kuma a bincika tsibirin; Ko da yake ilimi zai yawaita kuma hikima ta zama dala, duk da haka kowane rai zai rayu daga rana, kuma ruhun ɗan adam ba zai taɓa shiga ciki ba.
    bacewa. A cikin ƙasa, a cikin shekara, a cikin yini a wuri, jiki da rai za su rabu. Babu korafi, babu uzuri, babu daukaka kara, babu lauya, lokacin da rayukanmu za su amsa gida - kiran Allah. Kyakykyawa ga mummuna kasa, tsayi ga ƙura a ƙasa, ƙura ta koma ƙura, amma rai yana tashi. Wasan kwaikwayo na ƙarshe shine marigayin ya zauna cikin nutsuwa kamar yana raye a ƙarƙashin kalmar "Obituary" kuma a karrama shi da '' ''Late'' mai taken harafi 4 wanda ya biyo bayan sunansa har abada, don gaya wa duk mutumin da ya iya karantawa. cewa ya taba zama mazaunin wannan kasa mai faci. Mu masu rauni ne kuma masu iyaka. Mu duka tsuntsaye ne. An ba mu amma da ɗaukaka mai wucewa.
    Mai karatu na mai tawali'u, tashi, rana na faɗuwa, duhu yana zuwa, ka yi amfani da damarka. Ya kasance addini duk lokacin, yanzu lokaci yayi don ceto na gaskiya, yanzu shine sanya tsarkin zuciyar ku. Yi rajista don sama alhali ceto yana da arha kuma ruhun ku yana shirye.
    Ver libro
  • Spiritual colours and their meanings - Why God still Speaks Through Dreams and visions - HAUSA EDITION - School of the Holy Spirit Series 4 of 12 Stage 1 of 3 - cover

    Spiritual colours and their...

    LaFAMCALL, Lambert Okafor

    • 0
    • 0
    • 0
    Launuka na Ruhaniya da ma'anarsu - Me yasa har yanzu Allah ke Magana Ta Mafarki da wahayi
    
    Makarantar Ruhu Mai Tsarki Series 4 of 12, Stage 1 of 3
    
    A cikin mafarkin Makarantar Ruhu Mai Tsarki, wani al'amari mai ban sha'awa shine na Launuka na ruhaniya! Mutane suna ganin launuka a cikin mafarki, yayin da Allah yake amfani da waɗannan don koyar da mu kuma ya ba mu saƙonni, don haka ya zama dole mu san ma'anar waɗannan launuka.
    Allah ya kasance yana sha'awar launuka. A cikin Fitowa 28:1-6, Allah ya gaya wa Musa ya yi wa Haruna, babban firist tufafi masu tsarki, kuma ya ba shi takamaiman umarni game da launuka.
    Za su yi wa ɗan'uwanka Haruna da 'ya'yansa riguna domin su yi mini hidima a matsayin firist.
    A yau, har yanzu Allah yana magana game da launuka, wannan lokacin launuka na ruhaniya ta wurin, don haka dole ne mu san ma'anarsu. Launuka na ruhaniya sune launuka da muke gani a cikin mafarkinmu. Ba muna magana ne game da launuka na zahiri da muke da su a cikin tufafi da sauran wurare ba. Babu laifi a cikin kowane launi na zahiri, kamar yadda muka sani. Muna magana ne kawai game da muhimmancin ruhaniya na launukan da Allah ya kawo don ya koya mana cikin mafarkai da wahayi, a Makarantar Ruhu Mai Tsarki. Kada mu yi ƙoƙari mu yi amfani da waɗannan tattaunawa a kan launuka na zahiri na riguna da sauran kayan da muke da su. Ba wannan ba ne manufar.
    Ver libro
  • Spiritual Reflections Hausa Translation - English To Hausa Translation - cover

    Spiritual Reflections Hausa...

    Ken Luball

    • 0
    • 0
    • 0
    ”Tunanunnukan Ruhaniya: Littafi Game da Farkawa da Wayewa” littafi ne na wakoki, wanda ya ƙunshi wakoki 200 na Ruhaniya kyauta. Waɗannan waƙoƙin sun haɗa da tunanin da aka gani a cikin litattafai na ruhaniya guda huɗu a cikin “Jerin Litattafai Huɗu Na Farkawa”, ban da wasu da yawa da ba a buga ba tukunna. Babban jigon waɗannan waƙoƙi shi ne Ruhaniya, kowanne yana misalta bangarori daban-daban na “Farkawa” da “Wayewa”.
    Tunanunnukan na Ruhaniya: Littafin Farkawa da Wayewa littafi ne na wakoki, wanda ya kunshi kasidu 200 na ruhi kyauta. Waɗannan waƙoƙin sun haɗa da tunanin da aka gani a cikin litattafai na ruhaniya guda huɗu a cikin Jerin Litattafai huɗu na Farkawa, ban da wasu da yawa da ba a buga ba tukuna. Jigon wa]annan waƙoƙi shi ne Ruhaniya, kowanne yana misalta ɓangarori daban-daban na tsarin Farkawa da Wayewa. Ba su da addini, a'a, tunani ne na yau da kullum na ruhaniya game da wayewar ruhaniya. Ruhaniya ita ce imani akwai wani yanki na Ubangiji (Ruhi ko Rai) a cikin kowace rayuwa kuma, saboda wannan, kowace rayuwa tana da Muhimmanci, Daidaito, da Haɗaka. Burina na rubuta duka littattafai guda huɗu a cikin Jerin Litattafai huɗu na Farkawa da kuma wannan littafin waƙa, shine in yi ƙoƙarin farkarwa da taimaka wa wasu, waɗanda suka farka, su ƙara fahimtar menene Wayewa, don haka Tafiya ta Rayuwa za ta iya zama da cikakkiyar fahimta.
    PUBLISHER: TEKTIME
    Ver libro
  • WHOSE IMAGE ARE YOU? - Showing you how to obtain real deliverance peace and progress in your life without unnecessary struggles - HAUSA EDITION - School of the Holy Spirit Series 2 of 12 - cover

    WHOSE IMAGE ARE YOU? - Showing...

    LaFAMCALL, Lambert Okafor

    • 0
    • 0
    • 0
    SIFFOFIN WANENE KAI? Nuna muku yadda ake samun ceto na gaske, zaman lafiya da ci gaba a rayuwarku, ba tare da gwagwarmayar da ba dole ba - NEW EDITION
    ;
    Ubangiji Allah yana so mu sani cewa akwai cikakkiyar warkarwa da kubuta cikin sunan Yesu da kuma ta jininsa. Akwai babban zaman lafiya, farin ciki, ci gaba, nasara, maidowa ga mutanen Allah.
    Amma yadda muke bi wajen neman wadannan abubuwa (ceto, ci gaba, da sauransu) a kwanakin nan ba abin farantawa Allah rai ba ne. Mun watsar da saukin da ke cikin Almasihu, kuma mun maye gurbinsa da karkiyar addini mai nauyi. Kubuta na kyauta, wanda ke da sauƙin samu ta wurin Almasihu, ba ze zama kuma ba. An maye gurbinsa da wani nau'in ceto, ceton addini, wanda yake da wahala da tsada. Mutane suna biyan kuɗi da yawa, suna yin azumi da yawa, suna azabtar da kansu sosai duk a ƙoƙarinsu na samun kuɓuta. A ƙarshe, ba a isar da su da gaske ba! Matsalolinsu na nan a tare da su, ko ma sun yi muni.
    Manufar wannan littafi ita ce dawo da mu zuwa hanya mai sauƙi da yanci na samun cikakkiyar kuɓuta cikin Almasihu, ba tare da dukan gwagwarmayar addini da matsalolin da mutane suka dora mu ba.
    Waɗanda suka gwada hanyoyi masu sauƙi na Kristi, waɗanda ke cikin wannan littafin, sun yi mamakin yadda Allah zai iya sake yin abubuwa da sauri a cikin rayuwarsu, ba tare da ƙarin farashi ba, ba tare da gwagwarmaya ba.
    Bari Allah ya yi amfani da wannan littafin don ya taimaka ya kawo ku cikin cikakkiyar kuɓuta da ci gaba, waɗanda ya same mu cikin Almasihu Yesu.
    Ma'aikatun LaFAMCALL
    Ver libro
  • The Glorious Arrest of a Family - HAUSA EDITION - School of the Holy Spirit Series 8 of 12 Stage 1 of 3 - cover

    The Glorious Arrest of a Family...

    Lambert Okafor

    • 0
    • 0
    • 0
    Girman Kamun Iyali
    
    Gaban Ubangiji ya bayyana a gabansu a cikin gidansu kuma ya yi kwana uku. A rana ta uku Allah ya canza rayuwar kowa a cikin iyali, har da ta baƙo! Ya nuna musu manyan asirai da abubuwan da za su faru nan ba da jimawa ba a duniya; Sai ya ce su “je ku gaya wa kowa” abin da suka gani. Kafin wannan taron Mista & Mrs. Okafor ba su da ɗan lokaci ko kaɗan don abubuwan Allah. A yau labarin ya sha bamban. "Ƙarshen kowane abu yana nan kuma dole ne mu taimaka wa mutane," in ji marubucin.
    "...Wannan sakon yana da jan hankali, ƙauna, har ƙasa da GAGGAWA... Ina ba ku shawarar wannan littafin don karantawa da ... don ɗaukar matakan da suka dace."
    Ver libro
  • Hajji Da Umrah A Saukake - cover

    Hajji Da Umrah A Saukake

    Dalhatu Zariya Dahiru Muhammadu

    • 0
    • 0
    • 0
    Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna yabon Sa muna neman taimakon Sa kuma muna neman gafarar Sa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da sharrin miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, haka duk wanda Ya batar babu mai shiryar dashi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai bashi da abokin tarayya. Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne. Allah shi yi dadin tsira da albarka ga Manzon Sa Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da duk wanda yabi hanyar su da kyautatawa har ranar tashin kiyama. Bayan haka hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar kuma dukkanin wata bauta a musulunce ba a karbar ta sai anyi ta bisa ilmi kuma bisa koyarwar Manzon Allah (SAW). Manzon Allah yace: “kuzu anni manasika kum” (Ku riki salon aikin hajjin ku daga gareni). “Hajji da Umrah a Saukake” littafi ne dana rubuta shi domin yin bayani game da aikin Hajji da Umrah kamar yadda Manzon Allah ya koyar kuma ya karantar. Na rubuta littafinne da niyyar karantar da alhazai maniyyata aikin hajji, da daliban ilmi da sauran al’ummar musulmi baki daya. Littafin na kasa shi ne bisa babi hudu. Babi na daya zuwa na uku na tattauna ne akan sharudda, rukunai, nau’ukan aikin hajji da yadda ake yin kowane daya daga cikin au’ukan hajjin da abubuwan dake bata hajji. Da kuma muhimman hukunce-hukuncen da suka shafi mata kadai. Sannan babi na hudu kuma na tattauna ne akan ziyara zuwa Madina tare da ladubban ziyarar. Ina rokon Allah madaukakin sarki Ya gafarta wa duk wanda ya karanta wannan littafin, Ya datar dashi sunna da shiriyar manzon Allah (SAW), ya kuma karbe shi gareni a matsayin hidima ga addinin sa. Kuma Allah Ya sakawa wadanda suka taimaka wannan littafi ya tabbata da gidan Aljanna.
    Ver libro